Kante ya yi rauni a karawa da Bulgaria

Asalin hoton, Getty Images
An wallafa
Dan wasan Chelsea, N'Golo Kante ya yi rauni a lokacin da Faransa ta fafata da Bulgeria a wasan shiga gasar cin kofin duniya da Rasha za ta karbi bakunci a 2018.
Faransa ce ta doke Bulgaria daya mai ban haushi a fafatawar, kuma dan wasan Juventus Blaise Matuidi ne ya ci kwallon, daga baya aka sauya Kante daga karawar a minti na 34.
Faransa ce ke mataki na daya a kan teburin farko a wasannin nahiyar Turai da maki 20, sai Sweden wacce ta casa Luxembourg 8-0 ta biyu da maki 19.
Nasarar da Faransa ta yi ita ce ta 42 da kocin tawagar kasar, Didier Deschamps ya yi tun lokacin da ya karbi aikin daga hannun Laurent Blanc a 2012.























