Ingila ta hada maki 26 a rukuni na shida

Asalin hoton, Getty Images
An wallafa
Tawagar kwallon kafa ta Lithuania ta yi rashin nasara har gida da ci daya mai ban haushi a hannun Ingila a wasan shiga gasar cin kofin duniya da suka yi a ranar Lahadi.
Harry Kane ne ya ci kwallon kuma na tara a wasa biyar da ya buga wa Tottenham da Ingila, bayan da Ovidijus Verbickus ya yi wa Dele Alli keta.
Ingila ta buga karawar da sabbin 'yan wasa ganin cewar tuni ta samu tikitin shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018.
Ingila ba ta yi rashin nasara a wasannin shiga gasar cin kofin duniya ko ta Turai ba tun a shekarar 2009.























