Ingila ta ci kofin duniya na matasa 'yan 17

Asalin hoton, Getty Images
An wallafa
Tawagar kwallon kafa ta Ingila ta yi nasarar lashe kofin matasa 'yan kasa da shekara 17, bayan da ta casa Spaniya da ci 5-2.
Tun farko Spaniya ta ci kwallo biyu ta hannun dan wasan Barcelona Sergio Gomez, sai dak kafin hutu Ingila ta zare daya ta hannun Rhian Brewster kuma na takwas da ya ci a gasar.
Daga nan ne Ingila ta samu kwarin gwiwa ta farke ta hannun Morgan Gibbs Wwhite wasa ya koma 2-2.
Ingila ta kara cin kwallo biyu ta hannun Phil Fodaen, sannan Marc Guehi ya ci na biyar.
Tawagar kwallon kafar Ingila ce ta lashe kofin duniya na matasa 'yan 20 da aka yi a watan Yuni.























