Aminu Langa-Langa ya buge na Abata Mai

An dambata da dama a fafatawar da aka yi a gidan wasa na Ali Zuma da ke unguwar Dei-Dei a Abuja, Nigeria a safiyar Lahadi.
Daga cikin wasannin da aka yi har da wanda Aminu Shagon Langa-Langa daga Arewa ya buge Shagon Abata Mai daga Kudu a turmi farko.
Sai dai kuma Bahagon Aleka ne daga Kudu ya fara doke Sani Mai Kifi daga Arewa a turmin farko a wasan da aka fara a safiyar Lahadin.
Damben Autan Horo daga Arewa da Autan Dogon Aleka daga Kudu canjaras aka yi, haka ma wasa tsakanin Usha daga Arewa da Shagon Abata Mai daga Kudu babu wanda ya fadi.
Karawar da aka yi turmi uku tsakanin Bahagon Balan Gada daga Arewa da Dogon Aleka daga Kudu babu kisa alkalin wasa Tirabula ya raba su.
Sai aka dambata a wasan da Shagon Sama'ila daga Kudu ya yi nasara a kan Shagon Lawwalin Gusau daga Arewa a turmin farko.
Damben Shagon Fanteka daga Kudu da Shagon Bala Dan Zuru daga Arewa babu kisa, haka ma wasa tsakanin Shagon Shagon Lawwalin Gusau daga Arewa da Dan Abata Mai babu kisa.
Wasan daf da karshe da aka dambata kuwa Shagon Nuran Dogon Sani ne daga Arewa ya buge Shagon Autan Faya daga Kudu a turmi na biyu.



























