Barcelona ta gagara a gasar La Liga ta bana

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Mohammed Abdu
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
- An wallafa
Kungiyar Barcelona ta ci gaba da zama ta daya a kan teburin La Ligar Spaniya, bayan da ta kammala wasannin mako na 10 a karshen sati.
Barcelona ta ci wasa tara ta yi canjaras a karawa da ta tashi kunnen doki 1-1 a gidan Atletico Madrid a ranar 14 ga watan Oktoba.
Hakan ya sa kungiyar ta hada maki 28 kuma kwallo 28 ta ci inda Lionel Messi ya ci 12 daga ciki, sannan aka zura mata uku a ragarta tun fara kakar La Ligar shekarar nan.
Barcelona za ta buga wasan mako na 11 a ranar 4 ga watan Nuwamba, inda za ta karbi bakuncin Sevilla a Nou Camp.
Sai dai kafin nan kungiyar za ta buga gasar cin kofin Zakarun Turai da inda za ta ziyarci Olympiacos a wasan cikin rukuni, kuma Barcelona ce ke kan gaba a rukuni na hudun da maki tara.























