Man United za ta karbi bakuncin Benfica

Champions League
Bayanan hoto, Manchester United tana da maki tara a wasa uku da ta buga a gasar cin kofin Zakarun Turai a wasan rukunin farko
An wallafa

Manchester United za ta kara da Benfica a gasar cin Kofin Zakarun Turai wasan cikin rukunin farko da za su kece raini a ranar Talata a Old Trafford.

A makon jiya ne United ta ci Benfica daya mai ban haushi a Portugal kuma Marcus Rashford ne ya ci kwallo bayan da aka koma zagaye na biyu a karawar.

Kuma Manchester United da Benfica sun kara a gasar cin kofin Zakarun Turai sau 10, inda United ta ci wasa bakwai, suka yi canjaras biyu, Benfica ta ci wasa daya.

Daya wasan rukunin farkon za a yi ne tsakanin FC Basel da CSKA Moscow a Switzerland.

United ce ke mataki na daya a rukunin farko da maki tara sai Basel mai maki shida, yayin da CSKA Moscow keda maki uku, ita kuwa Benfica ba ta da maki ko daya.