Watakila Kane ya buga wasa da Madrid — Pochetino

Tottenham
Bayanan hoto, Kane ya ci kwallo biyar a wasa uku da ya buga a gasar cin kofin Zakarun Turai
An wallafa

Kocin Tottenham, Mauricio Pochettino yana da tabbacin cewar Harry Kane zai murmure domin buga gasar Zakarun Turai da za su kara da Real Madrid a ranar Laraba.

Kane ya ci wa Tottenham kwallo 13 a wasa 12 da ya buga wa kungiyar a bana, amma bai buga karawar da Manchester United ta doke su daya mai ban haushi a ranar Asabar a Premier ba.

Dan wasan ya buga atisaye a ranar Talata ana kuma sa ran zai iya fuskantar Real Madrid wacce suka tashi 1-1 a fafatawar da suka yi a Bernabeu.

Pochettino ya ce da sunan Kane a cikin wadanda za su kara da Madrid, kuma zai iya buga wasan amma ba shi da tabbaci dari bisa dari cewar zai saka shi a gumurzun.

Tottenham da Real Madrid suna mataki na daya da maki bakwai, sai Borussia Dortmund da Apoel Nicosia da suke biye da su.