Italiya ta kori kocinta Giampiero Ventura

Italy
Bayanan hoto, Giampiero Ventura ya yi aikin wata 17 a tawagar kwallon kafar Italiya
An wallafa

Hukumar kwallon kafa ta Italiya ta sallami koci Giampiero Ventura, bayan da ya kasa kai ta gasar cin kofin duniya a karon farko da ta kasa zuwa tun 1958.

Italiya ta yi rashin nasara a hannun Sweden da ci daya mai ban haushi, sannan suka tashi babu ci a Milan, wanda hakan ya kawo karshen aikin Ventura mai shekara 69, wata 17 da ya ja ragamar Italiya.

Sai dai kuma Ventura ya ce tarihinsa da ya kafa a tawagar ta Italiya, daya ne daga cikin wanda ya fi fice tun bayan shekara 40.

Kocin ya ce wasa biyu kacal ya yi rashin nasara a kusan shekara biyu da ya ja ragamar Italiya a hirar da ya yi da 'yan jarida tun kafin hukumar ta sallame shi daga aikin.

Ventura ya maye gurbin Antonio Conte a watan Yunin 2016, ya kuma samu maki daya daga shida da ya kamata a karawa da ya yi da Spaniya da canjaras da Macedonia a wasan shiga gasar cin Kofin duniya.