An bukaci magoya bayan West Ham su daina kiran lambar agaji ta 'yansanda kan rashin nasara

Asalin hoton, Getty Images
An bukaci magoya bayan West Ham su daina kiran lambar waya ta neman agaji ta 'yan sanda ta 999 domin korafi bayan da aka kara doke kungiyar tasu a gasar Premier ranar Lahadi.
Ofishin 'yan sanda na Essex ya aiki da wani sako ta shafin Twitter inda yake gargadi cewa ba za a lamunta da yadda magoya bayan kungiyar ke buga lambar waya ta neman agaji ba, ta 999, inda suke cewa an sake doke West Ham, ba su san abin da za su yi ba.
'yan sandan sun kara bayani da cewa kiran wannan lamabar waya ta 999 a game da doke West Ham bata lokaci ne kawai.
A ranar Lahadi Watford da ta karbi bakuncinsu ta doke su 2-0 a wasansu na ,ako na 12 na gasar Premier.
Sakamakon ya sa kungiyar wadda tsohon kociyan Manchester United David Moyes ya fara jagoranta a karawar ta yi wasa biyar ba tare da nasara ba a gasar ta Premier, kuma ta kasance cikin rukunin kungiyoyi uku da ke cikin hadarin faduwa daga gasar, inda take matsayi na 18 da maki tara, a sakamakon nasara biyu kawai a wasa 12.
Kwallaye biyu da Will Hughes da Richarlison suka zura a ragar West Ham din sun sa wasan farko da Moyes ke jagorantar kungiyar bayan da ya maye gurbin Slaven Bilic ya zo masa da sammatsi.

Asalin hoton, Getty Images
Magoya bayan Hammers din sun sanya wani babban kyalle mai dauke da sakon neman a rushe hukumar gudanarwar kungiyar, a lokacin karawar tasu da Watford.























