Kofin Zakarun Turai: Dortmund ta dawo da Aubameyang

Pierre-Emerick Aubameyang lokacin haduwarsu da Tottenham a Wimbley
Bayanan hoto, Alkalin wasa ya yi kuskuren hana kwallon da Pierre-Emerick Aubameyang ya ci a haduwarsu da Tottenham a Wembley
An wallafa

Borussia Dortmund ta tabbatar da cewa ta dawo da dan wasanta na gaba na kasar Gabon Pierre-Emerick Aubameyang bayan dakatar da shi da ta yi kwanan nan, domin hukunta shi kan rashin da'a.

A yanzu kenan zai yi wa kungiyar ta Jamus wasa a karawar da za ta yi a gidanta gobe Talata da Tottenham a gasar cin kofin Zakarun Turai.

Dan wasan bai taka wa Dortmund leda ba a karawar da Stuttgart ta doke su 2-1 a gasar Jamus ta Bundesliga, ranar Juma'a a matsayin horon da aka yi masa na zuwa filin atisaye latti, da kuma hoton bidiyon da ya dauka a lokacin atisaye, wanda bai yi shi da izini ba.

Kungiyar za ta zaku ta ga dan wasan wanda ya ci kwallo 15 a wasa 12 na farko a kakar nan, ya dawo kan ganiyarsa ta daga raga, wanda rabonsa da haka tun ranar 14 ga watan Oktoba.

Dortmund na matsayi na uku ne a rukuninsu na takwas (Group H), a gasar ta Zakarun Turai, wanda hakan ya sa dole sai ta doke Tottenham ta daya, wadda tuni ta tsallake zuwa mataki na gaba, kuma ta yi fatan Real Madrid ta kasa yin nasara a karawarta da APOEL ta Cyprus a ranar Talatar (gobe), domin ta ci gaba da kasancewa da 'yar damarta ta kaiwa zagayen 'yan 16.

Wasannin Zakarun Turai na ranar Talata;

Spartak Moskva da Maribor

Beşiktaş da Porto

Sevilla da Liverpool

Manchester City da Feyenoord

Napoli da Shakhtar Donetsk

Monaco da RB Leipzig

APOEL da Real Madrid

Borussia Dortmund da Tottenham Hotspur

A ranar Laraba ne kuma za a yi sauran wasannin gasar guda takwas kamar haka;

CSKA Moskva da Benfica

Qarabağ da Chelsea

Basel da Manchester United

Anderlecht da Bayern München

PSG da Celtic

Atlético Madrid da Roma

Juventus da Barcelona da

Sporting CP da Olympiakos Piraeus