Damben Boksin: George Groves zai kara da Eubank a Fabrairu

Asalin hoton, Reuters
Zakaran da ke rike da kambin damben boksin na ajin matsakaita nauyi na hukumar WBA George Groves zai yi damben kare kambin da Chris Eubank Jr a filin wasa na Manchester Arena ranar 17 ga watan Fabrairu.
Zakaran yana son a yi karawarsu ta damben kusa da na karshe na gasar WBSS (World Boxing Super Series) a wani filin wasan kwallon kafa a garinsa, Landan.
Wannan zai kasance lokaci na farko da Groves zai yi dambe a filin Manchester Arena tun lokacin dambensa da carl Froch a 2013, wanda aka yi takaddama kan rashin nasarar da aka ba shi.
Haka kuma karawar za ta kasance ta farko da 'yan damben boksin din Groves da Chris Eubank.
A watan da ya gabata Groves ya doke Jamie Cox a dambensa na farko na kare kambinsa, a wasan dab da na kusa da karshe na gasar ta Super Series a filin Wembley Arena.
Shi kuwa abokin karawar tasa Eubank ya zo wannan mataki ne na damben kusa da na karshen bayan da ya doke Avni Yildirim na Turkiyya a Jamus.
Dan dambe na uku na Birtaniya Callum Smith, zai fafata da Jurgen Brahmer na Jamus a daya damben kusa da na karshen, a wata rana da filin da ba a bayyana ba kawo yanzu.
Ita dai wannan gasar damben boksin ta WBSS kusan ana daukarta kamar gasar cin kofin zakaru na damben boksin.
Duk wanda ya yi nasara a sabuwar gasar zai karbi dala mliyan 50 da kuma kofi wanda aka sa masa sunan Muhammad Ali.
Gasar ta kunshi damben ajin nauyi biyu da na manyan matsakaita nauyi (super-middleweights) da kuma na gaba da shi (cruiserweight).
A kowannensu 'yan dambe takwas za su fafata daga matakin dab da na kusa da karshe har zuwa matakin karshe da za a samu wadanda za su zama zakaru a bangarorin biyu.



























