Kofin Zakarun Turai: Manchester City ta doke Feyenoord 1-0

Raheem Sterling lokacin da ya daga ragar Feyenoord
Bayanan hoto, Raheem Sterling ya ci bal dinsa ta 11 a bana a wasan da City ta doke Feyenoord
An wallafa

Manchester City ta zama ta daya a rukuninsu na shida ( Group F) na gasar kofin Zakarun Turai bayan da Raheem Sterling ya ci mata kwallo a kusan karshen wasan, minti na 88 a karawarta da zakarun Holland Feyenoord a Etihad.

Kasancewar Napoli ta doke ta biyu a rukunin Shakhtar Donetsk 3-0, hakan zai sa City ta je Ukraine wasanta na gaba ranar shida ga watan Disamba, hankali kwance sanin cewa ko da an doke ta ba za ta rasa damar wasan tsallakawa matakin gaba ba, na 'yan 16, wanda za ta yi a gida. Ko da yake masu rike da kofi Real Madrid na mata barazana.

Sakamakon na ranar Talata ya sa Guardiola ya hutar da wasu 'yan wasan, saboda karawarsu ta gaba ta Premier a gidan abokan hamayyarsu kuma masu binsu a tebur, manchester United.

Wasansu na karshe na rukunin na gasar ta zakaraun Turai za su yi shi ne ba tare da gwanin dan wasansu na tsakiya ba Kevin de Bruyne , bayan da dan wasan na Belgium ya samu katin gargadi na biyu, wanda hakan zai sa ya rasa wasa daya.

Bayan wasa biyar yanzu Manchester City tana ta daya da maki 15, Shakhtar Donetsk na bi mata da maki tara, sai napoli mai shida yayin da Feyenoord ba ta da ko daya.