Zakarun Turai: Juventus da Barcelona 0-0, PSG ta yi wa Celtic zazzaga

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona ta samu zuwa mataki na gaba na kungiyoyi 16 a gasar zakarun Turai duk da canjaras din da ta yi, ba ci a karo na biyu a wasan rukuni, da Juventus.
Duk yadda ta kasance a gaba Barca wadda take da maki 11 yanzu za ta kare a matsayin ta farko a rukuni na hudu, (Group D), ko da Juventus mai maki takwas a yanzu ta ci wasanta na gaba, ita kuma an doke ta, saboda tarihin nasarar da take da a kan zakarun na Italiya.
Sporting Lisbon, wadda za ta kara da Barcelona a Nou Camp ranar biyar ga watan Disamba, tana da damar zuwa mataki na gaba a gasar bayan da ta doke ta karshe a rukunin, Olympiakos ta Girka, da ci 3-0.
Ga alama Barca ta dan hutar da Messi ne a wasan wanda sai daga baya ya shigo ya canji tsohon dan wasan Everton Gerard Deulofeu a minti na 56, saboda karon-battarta na ranar Lahadi na La Liga, da Valencia ta biyu a tebur.
Wasan rukuni na biyu (Group B) PSG da Celtic

Asalin hoton, Rex Features
Paris St-Germain ta casa bakinta Celtic da ci bakwai da daya a wasan da aka yi a gidan zakarun Faransan, Parc de Princes.
Celtic ce ta fara bude ci ta hannun Moussa Dembele, minti daya kacal da shiga fili, daga nan ne kuma sai masu masaukin suka farga, suka fara ruwan kwallo.
Neymar ya ci biyu tun da farko, kafin kuma ya samar da dama ga Edinson Cavani, ya ci ta uku, sannan Kylian Mbappe ya ci ta hudu kafin tafiya hutun rabin lokaci.

Asalin hoton, Others
Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci Marco Verratti da Cavani da kuma Dani Alves suka kara ci a tsakanin minti biyar biyar, lamarin da ya bata lissafin Celtic gaba daya.
Nasarar ita ce mafi girma da PSG ta taba yi a gasar zakarun Turai, wadda daman a karon farko ta doke Celtic a Glasgow da ci 5-0.
Zakaran na Scotland har yanzu suna da damar kammalawa a matsayi na uku a rukunin (Group B), inda za su samu damar zuwa gasar kofin zakarun Turai na Europa, inda ta karshe a rukunin Anderlecht ta sha kashi a hannun Bayern Munich 2-1.
PSG ce ta daya a rukunin da maki 15, Baeryn Munich na bi mata baya da 12, yayin da Celtic ta uku take da maki uku, ita kuwa Anderlecht ba ta da maki ko daya, a wasa biyar.



























