Dambe: 'Da wuya kudi su bar McGregor ya dawo fage'

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban hukumar damben hannu da kafa ta duniya, UFC, Dana White ya ce hukumar na kokarin kulla wata sabuwar yarjejeniya da zakaran damben, dan Ireland Conor McGregor, amma kuma ya ce kila ba zai sake dawowa fage ba saboda ya samu kudi.
McGregor bai yi dambe ba a karkashin hukumar tun bayan da ya yi wa Eddie Alvarez dukan kawo-wuka a watan Nuwamba na 2016.
Shugaban yana ganin tun da McGregor yanzu ya zama daya daga cikin attajiran 'yan wasa a duniya bayan damben boksin din da ya yi da Floyd Mayweather Jr a farkon shekaran nan, akwai yuwuwar ba zai sake dambe ba a karkashin hukumar.
Da yake jawabi a hedikwatar hukumar a Las Vegas White ya ce, kila Conor ba zai sake damben ba, saboda ya mallaki dala miliyan 100, ''domin ina da mutanen da suka samu kudin da bai kai haka ba, wadanda lauyoyi ne, kuma duk tsawon rayuwarsu makaranta suka sani, amma yanzu sun bar aiki.''























