Pochettino ya dace da United -— Rooney

Asalin hoton, Getty Images
Wayne Rooney ya ce Mauricio Pochettino yana da dukkan kwarewar da Manchester United ke bukata domin ya horar da 'yan wasanta tamaula a badi.
An dade ana alakanta Pochetino da United tun bayan da aka kori Jose Mourinho a Old Trafford a watan Disamba, inda Rooney ya ce kwazon da kocin ya yi a Tottenham ya ga dacewarsa.
Bayan da aka sallami Mourinho ne United ta nada tsohon dan wasanta Ole Gunnar Solskjaer kocin rikon kwarya, inda ya ci wasa bakwai a karawa bakwai da ya ja ragamar kungiyar.
Rooney tsohon dan wasan Manchester United ya ce ya kamata a bai wa Ole damar nuna bajintarsa, idan kuma ya ci gaba da kokarin da yake a yanzu to sai a nada shi koci na dindindin.
Sai dai Rooney ya ce da shi ne ke da wuka da nama a yanke hukuncin daukar koci a Old Trafford lallai Pochettino zai dauka.
Rooney ya ci wa United kwallo 253 a wasa 559 da ya buga mata, tun bayan da ta dauko shi daga Everton a 2004.
Daga baya ya sake komawa Everton a kakar 2017, yanzu kuma yana murza-leda a DC United ta Amurka.























