Hotunan filin wasan Tottenham da aka gina kan ₦472b

An wallafa

Tottenham za ta fara buga wasan Firimiya ne a sabon filin wasan tare da Crystal Palace a ranar 3 ga watan Afrilu.

Tottenham stadium
Bayanan hoto, Sabon filin wasa na kungiyar Tottenham Hotspur ya lamushe zunzurutun kudi har fan biliyan dubu daya, kwatankwacin kusan rabin tiriliyon na naira
Tottenham stadium
Bayanan hoto, Ana yi wa filin wasan lakabi da "State of the art" a yanzu kafin a rada masa suna na dindin
Tottenham Stadium
Bayanan hoto, Filin wasan yana iya daukar 'yan kallo 62,062, wanda hakan ya sa ya zama mafi girma a birnin Landan kuma na biyu a gasar Firimiyar Ingila bayan Old Trafford
Harry Kane
Bayanan hoto, Hoton tauraron dan wasa Harry Kane ne aka sa a jikin gilashin kofar shiga filin wasan yana yi wa mutane maraba
Tottenham stadium
Bayanan hoto, Wannan shi ne abin da 'yan kallo za su tarar yayin da suka shiga ciki.
Tottenham players
Bayanan hoto, Tottenham ta bude filin ne da wasa tsakaninta da kungiyar Southampton a wasan Firimiya na 'yan kasa da shekara 18, inda ta yi nasara da 3-1
Tottenham stadium
Bayanan hoto, Za a fara buga wasan gasar Firimiya na farko a filin wasan a ranar 3 ga watan Afrilu, inda Tottenham za ta karbi bakuncin Crystal Palace
Tottenham stadium
Bayanan hoto, Ana iya nade ciyawar filin wasan domin buga wasan Rugby