Arsenal ta koma ta uku a teburin Premier

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal ta dare mataki na uku a teburin Premier League, bayan da ta doke Newcastle United 2-0 a karashen wasan mako na 32 da suka yi a Emitates ranar Litinin.
Arsenal ta ci kwallo ne ta hannun Aaron Ramsey saura minti 10 aje hutu, sannan ta kara na biyu ta hannun Alexandre Lacazette saura minti bakwai a tashi daga karawar.
Da wannan sakamakon Arsenal ta koma ta uku a kan teburin Premier da maki 63, cikin 'yan hudun farko da za su iya wakiltar Ingila a gasar Zakarun Turai ta Champions League a badi.
Arsenal tana buga gasar Europa League har ta kai karawar daf da na kusa da na karshe, inda za ta fafata da Napoli ranar Alhamis 11 ga watan Afirilu a Emirates.
Arsenal za ta ziyarci Everton a wasan mako na 33 a gasar ta Premier ranar 7 ga watan Afirilu a karawar da za su yi a Goodison Park.
Sauran wasannin da Arsenal za ta yi a Premier
Lahadi 7 Afirilu 2019
- Everton da Arsenal Goodison Park
Litinin 15 Afirilu 2019
- Watford da Arsenal Vicarage Road
Lahadi 21 Afirilu 2019
- Arsenal da Crystal Palace Emirates Stadium
Laraba 24 Afirilu 2019
- Wolves da Arsenal Molineux Stadium
Litinin 29 Afirilu 2019
- Leicester da Arsenal King Power Stadium
Asabar 4 Mayu 2019
- Arsenal da Brighton Emirates Stadium
Lahadi 12 Mayu 2019
- Burnley da Arsenal



























