Real za ta ziyarci Valencia a La Liga

Asalin hoton, Getty Images
Valencia za ta karbi bakuncin Real Madrid a wasan mako na 30 a gasar cin kofin La Liga da za su kara ranar Laraba.
A wasan farko da suka yi a Santiagio Bernabeu ranar 1 ga watan Disambar 2018 a bana, Madrid ce ta yi nasara da ci 2-0, inda Valencia ta fara cin kanta ta hannun Daniel Wass daga baya Lucas Vazquez ya ci kwallo na biyu.
A kakar bara da kungiyoyin biyu suka kara a La Liga, sun tashi 2-2 a wasan farko da aka yi a Bernabue ranar 27 ga watan Agustan 2017, inda Real ta ci karawa ta biyu 4-1 ranar 27 ga watan Janairun 2018.
Real Madrid tana ta uku a kan teburin La Liga da maki 57, yayin da Valencia tana ta bakwai da maki 43.
Wannan ne wasa na uku da Zinedine Zidane zai ja ragamar Real, bayan da ya karbi aikin horar da ita karo na biyu.
Madrid ta dauki Julen Lopetegui a matakin kocin kungiyar kan fara kakar bana, daga baya ta sallame shi ta nada Santiago Solari shi ma bai kai labari ba, inda Zidane ya maye gurbinsa.
Ajax ce ta fitar da Real mai rike da kofin zakarun Turai a wasan zagaye na biyu a bana, sannan Barcelona ta yi waje da Madrid a Copa Del Rey karawar daf da karshe.
Real Madrid tana ta uku a teburin La Liga da tazarar maki biyu tsakaninta da ta biyu Atletico Madid, sannan Barcelona ta daya ta ba ta tazarar maki 12.



























