Chelsea da Tottenham za su yi kwantan wasa

Chelsea Tottenham
    • Marubuci, Mohammed Abdu
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
  • An wallafa

Hukumar gudanar da gasar Premier ta tsayar da ranar Laraba, domin Chelsea da Tottenham su buga kwantan wasan da suke da shi.

Chelsea za ta karbi bakuncin Brighton & Hove Albion karawar kwantan wasan mako na 27 a gasar ta Premier.

Brighton da Chelsea sun fafata a wasannin bana ranar 16 ga watan Disambar 2018, inda kungiyar Stamford Bridge ta yi nasara da ci 2-1.

Ita kuwa Tottenham za ta karbi bakuncin Crystal Palace a karawar farko da za ta yi a sabon filinta a kwantan wasan mako na 31.

Kungiyoyin biyu sun fafata a Selhurst Park karo biyu a bana, inda aka ci Tottenham 1-0 a Premier ranar 10 ga watan Nuwambar 2018, sannan Palace ta fitar da Tottenham a FA Cup da ci 2-0 ranar 27 ga watan Janairun 2019.

Tottenham tana ta hudu a kan teburin Premier da maki 61, ita kuwa Chelsea tana ta shida da maki 60.

A cikin watan nan na Afirilu ne Tottenham za ta buga wasan daf da na kusa da na karshe da Manchester City a Champions League.

Ita kuwa Chelsea mai buga gasae Europa League za ta fafata ne da SK Slavia Prague a wasan daf da na kusa da na karshe.