Arsenal ta yi tuntube a Goodison Park.

Asalin hoton, Getty Images
Everton ta yi nasarar doke Arsenal da ci 1-0 a wasan mako na 33 da suka kara a gasar Premier ranar Lahadi a Goodison Park.
Phil Jagielka ne ya ci kwallon tun a minti na 10 da fara tamaula, kuma hakan ne ya bai wa Eveton maki uku rigis a karawar.
Wasa na uku a jere da Everton ta yi nasara kenan a gasar cin Kofin Premier, inda hakan ya sa ta hada maki 46 tana ta tara a kan teburi.
Ita kuwa Arsenal wadda take fatan kammala wasannin bana cikin 'yan hudun farko tana ta hudun da maki 63.
Arsenal ce kungiyar da kwallo ya shiga ragarta a wasannin da ta buga ba a gidanta ba kawo yanzu.
Rashin nasarar da Arsenal ta yi ya sa ba za ta koma ta uku a kan teburi ba, bayan karawar mako na 33, inda Tottenham ce ta ci gaba da zama a gurbin.
Yadda kungiyoyin suka murza-leda

Asalin hoton, BBC Sports
Rashin kokarin Arsenal a karawar da ta yi ba a gidanta ba:
- Arsenal ta yi rashin nasara a wasa bakwai daga 11 da ta buga a waje( Ta ci biyu da canajaras biyu da rashin nasara bakwai)
- Arsenal ce kungiyar da a gasar Premier bana kwallo ya shiga ragarta a dukkan fafatawar da ta yi a waje.
- A watan Agustan 1999 Richard Gough ya ci Southampton kwallo yana da shekara 37 da kwana 138, sai kuma Phil Jagielka da ya zura kwallo a ragar Arsenal yana da shekara 36 da kwana 233.
- Gylfi Sigurdson na Everton ya kai hari sau bakwai, fiye da wanda Arsenal ta kai a karawar.
- Everton ta yi nasara a wasa biyu a kan 'yan shidan farko a Premier, fiye da karawa 41 baya da ta yi da su, ( Ta ci biyu da canajaras 14 aka doke ta 25.
- Patrick Vieira a shekarar 1996-97 da Shkodran Mustafi a kakar 2016-17 kowanne ya karbi kadin gargadi sau 11 a PrenmierSai wannan kakar da Sokratis wanda ke da 10 kawo yanzu.



























