Afcon 2019: An hada Masar da DR Congo, Kamaru da Ghana

Asalin hoton, Reuters
Masar za ta hadu da DR Congo da Uganda da Zimbabwe a rukunin A, a gasar cin kofin Afika ta 2019.
Kamaru mai rike da kofin gasar na rukunin F tare da Ghana da Benin da kuma Guinea-Bissau.
Za a fafata ne a gasar a tsakanin ranar 21 ga Yuni zuwa 9 ga Yuli, bayan kammala kakar wasanni a Turai.
Hakan na nufin 'yan wasan Afirka da ke taka leda a Turai za su haska a gasar.
Gasar bana za ta kunshi kasashe 24, kuma karon farko ke nan da za a gudanar da gasar a lokacin bazara a turai maimakon watan Janairu zuwa Fabrairu da aka saba.
Morocco na rukunin D ne da ita da Ivory Coast da Afirka ta Kudu da kuma Namibia.
Za a fara fafaawa ne tsakanin Masar da Zimbabwe a ranar 21 ga Yuni a Cairo.
An hada Najeriya ne a rukunin B tare da Guinea da kuma sabbin shigowa a gasar Burundi da Madagascar.
Jadawalin gasar
Rukunin A: Masar, DR Congo, Uganda, Zimbabwe
Rukunin B: Najeriya, Guinea, Madagascar, Burundi
Rukunin C: Senegal, Algeria, Kenya, Tanzania
Rukunin D: Morocco, Ivory Coast, Afirka ta kudu, Namibia
Rukunin E: Tunisia, Mali, Mauritania, Angola
Rukunin F: Kamaru, Ghana, Benin, Guinea-Bissau



























