Man City ta jiyo kanshin kofin Premier

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City ta sake dare mataki na daya a kan teburin gasar Premier bana, bayan da ta doke Leicester City 1-0 a ranar Litinin.
City wadda ta karbi bakuncin Leicester a wasan mako na 37 a Etihad, ta ci kwallon ne ta hannun kyaftin dinta Vincent Kompany saura minti 20 a tashi daga wasan.
Wannan ne karo na uku da kungiyoyin suka fafata a bana, inda suka fara tashi 1-1 ranar 18 ga watan Disambar 2018 a League Cup.
Haka kuma sun fafata a wasan Premier a King Power ranar 26 ga watan Disambar 2018, inda Leicester City ta yi nasara da ci 2-1.
City na shirin lashe kofi uku a kakar bana, bayan da ta ci League Cup, za ta buga wasan karshe a kofin FA, sannan tana ta daya a kan teburin Premier.
A ranar Lahadi za a karkare wasannin Premier bana, kuma da zarar City ta yi nasara a kan Brighton za a mallaka mata kofin, kuma ita ce ke rike da na bara.
Yadda teburi yake bayan karawar mako na 37

Asalin hoton, BBC Sport
Wasannin da za a buga ranar Lahadi 12 Mayu 2019
- Fulham da Newcastle United
- Liverpool da Wolverhampton Wanderers
- Manchester United da Cardiff City
- Southampton da Huddersfield Town
- Tottenham da Everton
- Leicester City da Chelsea
- Watford da West Ham United
- Burnley da Arsenal FC Week: 38
- Crystal Palace da Bournemouth



























