Shugaban CAF ya 'kasance' a kasashe biyu a lokaci guda

Ahmad
Bayanan hoto, Ahmad ya fara jan ragamar hukumar Caf ne a watan Maris din 2017
An wallafa

Ana ci gaba da matsa wa Shugaban Hukumar kula da kwallon kafa ta Afirka (CAF) Ahmad lamba bayan hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta zarge shi da almundahana.

Wani bincike da BBC ta yi, ya gano cewa Ahmad ya karbi alawus kashi biyu, inda yake ikirarin ya kasance a kasashe biyu a lokaci guda a lokacin Gasar Cin Kofin Duniya a shekarar 2018.

Kamar yadda wasu takardun bincike suka bayyana, mataimakin shugaban Fifa ya karbi kudi har sau biyu daga hukumar CAF, inda ya ce ya yi aiki tsakanin ranakun 23 ga watan Yuni zuwa 1 ga watan Yuli.

A karon farko, takardun sun nuna cewa ya karbi alawus da ke cewa yana kasar Masar na wani dan lokaci - kafin daga bisani ya sanya hannu a wasu takardu da ke cewa yana Rasha ne a daidai wannan lokacin.

A matsayin mataimakin shugaban Fifa, da Ahmad ya karbi alawus na dala 450 daga Fifa a kowace rana wajen shirya gasar - wanda hakan yana nufin wata kila ya karbi kudin kwana tara a tsawon lokacin.

Hukumar CAF, wadda take da hedikwata a birnin Alkahira a Masar, ba ta da hurumi wajen shirya gasar.

Sai dai da hukumar CAF ta ce tana bincike a kan al'amarin kuma za ta bayyana wa "duniya abin da ta gano."

A watan Maris din 2017 ne Ahmad ya fara jan ragamar hukumar CAF kuma yanzu haka kwamitin da ke kula da da'a na Fifa da hukumar yaki da cin hanci ta kasar Faransa suna bincikensa kan zargin wata almundahana.

Sai dai Ahmad wanda dan kasar Madagascar ne ya musanta duka zarge-zargen.