Neymar, van de Beek, Mandzukic, Lukaku, Cahill a kasuwar sayen 'yan wasa

Donny van de Beek
Bayanan hoto, Donny van de Beek mai shekara 22 yana cikin tawagar Ajax da kai wasan kusa da na karshe a Champions League
An wallafa

Jaridar Sun ta ruwaito cewa Man United ta ki yarda da tayin da Real Madrid ta yi mata kan Paul Pogba, inda za ta hada da James Rodriguez a matsayin musaya.

Sai dai Real Madrid ta yanke shawarar daukar Donny van de Beek mai shekara 22 daga Ajax a maimakon Pogba, in ji rahoton Marca.

Jaridar Mail ta ruwaito cewa Manchester United ta amince ta biya albashin fan miliyan £6.2 duk shekara ga dan wasan Juventus Mario Mandzukic mai shekara 33.

United za ta dauke shi ne kan fan milyan £15 ko kuma ta yi musayarsa da Romelu Lukaku mai shekara 26 dan kasar Belgium.

Barcelona ta fasa daukar dan wasan Paris St-Germain kuma dan kasar Brazil wato Neymar mai shekara 27 a wannan kakar ta bana, a cewar rahoton Goal.com.

Sai dai shugaban kungiyar ta Barcelona ya nuna cewa kulob din zai iya kara sayo wani dan wasan bayan ta tabbatar da daukar matashin dan wasa Junior Firpo daga Real Betis. (Sport)

Manchester City ta shirya tsaf domin daukar dan wasan bayan Juventus Joao Cancelo mai shekara 25 kan fan miliyan £32 , inda shi kuma Danilo zai koma Juventus din. (Mail)

West Ham tana kokarin daukar dan wasa na biyar a hutun kakar bara amma ba za ta nemi Gary Cahill ba tsohon dan bayan Chelsea mai shekara 33. (Football.London)

Sai dai Crystal Palace na kokarin kulla yarjejeniya da dan wasan, inda za ta rika biyansa fan £75,000 duk mako. (Sun)

A karshe dai Virgil van Dijk na Liverpool ya sha yanka a wasan kofin kalubale na Community Shield tsakanin Liverpool da Manchester City ranar Lahadi.

Dan kasar Netherlands din ya yi wasa 65 a jere ba tare da wani dan wasa ya yanke shi ya wuce ba, kamar yadda Goal ta ruwaito.

Leicester City na tunanin daukar James Tarkowski mai shekara 26 daga Bournemouth ko kuma Nathan Ake domin maye gurbin Harry Maguire, wanda ya koma Manchester United. (Sky Sports)