'Yan wasan baya mafiya tsada a duniya

Asalin hoton, Getty Images
A ranar Litinin Manchester United ta mayar da Harry Maguire mai tsaron baya mafi tsada a duniya, bayan da ta sayi dan wasan tawagar Ingila daga Leicester City kan fan miliyan 80.
Ga jerin wadanda aka dauka mafiya tsada a tarihi a duniya:
Harry Maguire, fan miliyan 80, Leicester zuwa Manchester United (Agustan 2019)
Mai tsaron bayan tawagar Ingila shi ne kan gaba da Manchester United ta yi zawarci, bayan da masu tsaron bayan kungiyar ta yi kura-kurai a bara da ya kai ta kare ba tare da lashe kofi ba.
Hankalin Ole Gunnar Solskjaer ya kwanta ganin ya dauko mai tsaron baya da zai karfafa karfin United a kakar da za a fara ta bana ranar Juma'a.

Asalin hoton, Getty Images
Virgil van Dijk, fan miliyan 75, Southampton zuwa Liverpool (Janairun 2018)
Liverpool ta sayo dan kwallon tawagar Netherlands Van Dijk a matsayin mafi tsada a lokacin, kuma kwalliya ta biya kudin sabulu, inda Liverpool ta kai wasan karshe a Champions League sau biyu a jere.
Liverpool din ta lashe Champions League a kakar da aka kammala, bayan da ta doke Tottenham ta zama gwarzuwar Turai kuma karo na shida jumulla.

Asalin hoton, Getty Images
Lucas Hernandez, fan miliyan 68, Atletico Madrid zuwa Bayern Munich (Julin 2019)
Dan kwallon tawagar Faransa ya koma Spaniya tun yana da shekara hudu daga nan ya buga kwallo a matasan Atletico Madrid.
Hernandez ya lashe kofin duniya a 2018 a Rasha, ya kuma buga wa Atletico wasa sama da 100 daga nan ya koma buga gasar Bundesliga tare da Bayern Munich a bara.

Asalin hoton, Getty Images
Matthijs De Ligt, fan miliyan 67.5 (zai kai fan miliyan 77 da tsarabe-tsarabe), Ajax zuwa Juventus (Julin 2019)
De Ligt ya fara buga wa Ajax da tawagar kwallon kafar Netherlands tamaula yana da shekara 17, kuma nan da nan ya koma buga baya daga matakin mai wasa daga tsakiya.
De Ligt ya yi wa Ajax wasa sama da 100, ya kuma yi kyaftin a matasan kungiyar, ya kuma kai karawar daf da karshe a Champions League a bara daga nan ya koma Juventus a bana wata daya kafin ya cika shekara 20.

Asalin hoton, Getty Images
Aymeric Laporte, fan miliyan 57, Athletic Bilbao zuwa Manchester City (Janairun 2018)
Dan kwallon tawagar Faransa ya je Athletic Bilbao yana da shekara 16 da haihuwa.
Laporte ya buga wa Bilbao wasa sama da 200, inda Manchester City ta saye shi a matsayin mafi tsada a duniya a Janairun 2018.
Dan wasan ya lashe Premier League biyu a City da League Cup da kuma FA.



























