Ina Pogba, Moyes, Dybala, Khedira da Mourinho za su?

Paul Pogba
An wallafa

Juventus har yanzu ba ta cire tsammani ba kan burinta na karbo Paul Pogba daga Manchester United mai shekara 26. (Express)

Pogba ya ce ba zai raba kan 'yan wasan Manchester ba, saboda kudirinsa na son ficewa daga Old Trafford. (Mirror)

Jose Mourinho ya samu aiki a matsayin mai sharhi a kafar wasanni ta Sky Sports kuma zai fara sharhi ne a wasan ranar lahadi da tsoffin kungiyoyinsa biyu za su kara Manchester United da Chelsea. (Sky Sports)

Bayern Munich na dab da dauko dan wasan Croatia Ivan Perisic, mai shekara 30, daga Inter Milan.

Bangarorin biyu sun cimma yarjejeniya, inda dan wasan zai tafi a matsayin aro, amma da nufin sayensa kan kudi £23.5m. (Sky Italia via Sky Sports)

Tsohon kocin Everton da Manchester United David Moyes yana cikin jerin sunayen wadanda za a ba aikin horar da kungiyar David Beckham Inter Miami. (Mirror)

Dan wasanJuventus Paulo Dybala, mai shekara 25, na Argentina yana cikin tawagar kungiyar da za su buga wasan sada zumunci da Atletico Madrid a Stockholm duk da Paris St-Germainna sha'awar dan wasan.(Mail)

Juventus ta damu da dan wasanta na tsakiya dan kasar Jamus Sami Khedira bayan dan wasan mai shekara 32 ya yi watsi da tayin kungiyoyi da dama saboda yana jiran Arsenal ta taya shi. (Calciomercato via Sun)