Ko Man United za ta iya doke Wolves kuwa?

Asalin hoton, Getty Images
A ranar Litinin za a karkare wasannin mako na biyu a gasar cin kofin Premier, inda Wolverhampton za ta karbi bakuncin Manchester United a filin wasa na Molineux.
United ta hada maki uku a wasan farko a bana, bayan da ta ci Chelsea 4-0, ita kuwa Wolves maki daya take da shi, bayan da ta tashi wasa babu ci a gidan Leicester City.
A gasar bara United ta kasa doke Wolves a haduwa ukun da suka yi, inda ta yi rashin nasara a gidan Wolves da ci 2-1 sannan suka tashi 1-1 a gasar Premier.
Haka kuma a ranar 16 ga watan Maris, 2019 Wolverhampton ta fitar da United a gasar cin kofin kalubalen kasar, wato FA Cup.

Asalin hoton, Getty Images
Kokarin da Wolves ta yi a bara a gasar Premier shi ne ya sa ta kammala a mataki na bakwai, hakan ya bata damar buga wasannin cike gurbin shiga gasar Europa ta bana.
Kocin United, Ole Gunnar Solskjaer ya ce ya kwan da sanin Wolhampton wadda Nuno Espirito Santo ke jan raga kungiya ce mai tsauri, amma zai saka kaimi don samun maki maki uku.
Solskjaer ya ce ba kungiya ce da idan kana karawa da ita za ka dunga barin 'yan wasanta na wataya wa ba a fili, sannan sun kware wajen kai hare-hare, amma zai yi wasan da kwarin gwiwa.
Kocin na United ya kara da cewar ya yi murna da ya sayo Harry Maguire mai tsaron baya a matakin wanda ya fi kowa tsada daga Leicester City kan fam miliyan 80.
Mai horas da United ya ce kwalliya ta fara biyan kudin sabulu, domin dan wasan tawagar kwallon kafa ta Ingila mai shekara 26 ya taka rawar gani a wasan da United ta doke Chelsea 4-0 a Old Trafford.



























