Real ta ci wasa 283 a La Liga tare da Ramos

Ramos
An wallafa

Real Madrid ta fara gasar La Liga ta bana da kafar dama, bayan da ta je ta doke Celta Vigo 3-1 a wasan makon farko ranar Asabar.

Real ta ci kwallayen ta hanun Karim Benzema da Toni Kroos da kuma Lucas Vazquez, yayin da Celta ta zare daya daf da za a tashi daga wasan ta hannun Iker Losada.

Sergio Ramos ya buga wasan da Real ta yi a Balaidos, wanda shi ne na 283 da Madrid ta yi nasara a La Liga tare da kyaftin din nata.

Hakan ne ya sa ya yi kan-kan-kan da Gento a mataki na hudu a jerin 'yan Real Madrid da ta ci wasannin La Liga da dama a cikin fili.

Ramos ya yi wasa 420 aka ci karawa 283 da shi a La Liga, shi kuwa Gento ya yi wa Real fafatawa 427 aka ci wasa iri daya da na Ramos da shi a fili.

Wadan da ke kan gaba a yawan nasara a Real Madrid a La Liga sun hada da Sanchís wanda aka ci karawa 312 da shi a mataki na uku sai Raúl mai 327 na biyu da Casillas da aka ci wasan La Liga 334 yana tsaron raga.

Wannan ce kaka ta 15 da Ramos ke buga gasar La Liga a Real Madrid, kuma shi ne na bakwai a jerin 'yan wasan da suka buga wa kungiyar karawa da yawa.

Kyaftin din ya ci kwallo 59 a gasar ta La Liga a shekara 15 da yake buga wasannin, kuma a kakar 2016/17 ce ya fi zura kwallaye a gasar, wanda ya ci 7.

Ranar Juma'a 23 ga watan Agusta za a fara wasannin mako na biyu a La Liga, inda Real Madrid za ta karbi bakuncin Real Valladolid a Santiago Bernabeu ranar Asabar.