Liverpool vs Arsenal: Na daya da na biyu

Liverpool vs Arsenal
Bayanan hoto, Arsenal ba ta ci Liverpool ba a wasa takwas na baya-bayan nan
An wallafa

Da karfe 5:30 agogon Najeriya za a buga wasan Premier mako na uku tsakanin Liverpool da Arsenal - na daya da na biyu a saman teburi.

Labaran kulob din guda biyu

Mai tsaron raga Alisson zai ci gaba zama a benci domin ci gaba da jinyar raunin da ya samu a kafarsa. Adrian ne zai kama masu ragar.

Naby Keita da Nathaniel Clyne su ma ba za su buga ba, amma Dejan Lovren zai iya bugawa bayan ya dawo atasaye daga raunin da ya ji.

Kocin Arsenal Unai Emry zai iya amfani da dan wasansa mafi tsada a tarihin kulob din Nicolas Pepe a baki dayan wasan.

An yi wa Ozil da Xhaka gwajin lafiyar ko nza su iya buga wasan ganin cewa kowannensu bai dade da samun sauki ba daga raunin da suka ji.

Kociyoyi na cewa:

Kocin Liverpool Jurgen Klopp yana magana kan irin haramar da 'yan wasansa suke da ita:

"Kungiyata ta lashe kofin Zakarun Turai, saboda haka abin mamaki ne ma idan da ba su lashe shi ba.

"Abin dai ba zai wuce yadda 'yan wasa za su tallafa wa junansu ba a cikin fili, ba wai a wajen fili ba kawai."

Shi kuwa kocin Arsenal Unai Emry yana magana game da rashin sa'ar da kulob dinsa yake da ita kan manyan kungiyoyin Premier guda shida wato top six, wanda Liverpool tana ciki:

"Ya kamata mu kara kokari idan muna wasa da su. Maki uku za mu ci wanda ba za su ci ba.

"Bayan haka kuma kana bukatar ka kuma cin wasu maki ukun a kan wani kulob din daban. A wasa 38 da za mu yi a gida da waje za mu buga 19 ne tare da manyan kungiyoyi shida."

Tarihin wasa tsakanin kungiyoyin

Liverpool ba ta yi rashin nasara ba a wasa takwas na baya-bayan nan tsakaninta da Arsenal.

Arsenal ba ta yi nasara ba a wasa shida na baya-bayan nan a filin wasa na Anfield, sannan an zura mata kwallo biyu ko sama da haka a duka wasa shidan - kwallo 22 baki daya.

Wasa tsakaninsu shi ne wanda aka fi zura kwallaye a Premier, inda aka zura 155 cikin wasa 54. Sannan kuma an yi hat-tricks har sau shida.

An ci kwallo 53 a wasa 12 tsakanin kungiyoyin a dukkanin gasanni.