Lazio ta tsira da kyar a hannun Roma

Asalin hoton, Getty Images
An raba maki a wasan hamayya tsakanin Lazio da Roma a wasan mako na biyu a gasar Serie A da suka kara ranar Lahadi.
Roma ce ta fara cin kwallo ta hannun Aleksandar Kolarov a bugun fenariti, bayan da dan wasan Lazio, Sergej Milinkovic-Savic ya taba kwallo da hannu a da'ira ta 18.
Tun farkon take kwallo Ciro Immobile da kuma Joaquin Correa sun buga tamaula ta bugi turke, haka kuma Nicolo Zaniola ya taka-ledar da ya gagari Roma.
Lazio ta farke kwallo ne ta hannun Romero Alconchel, minti kadan bayan da aka koma hutu.
Mai masaukin baki wato Lazio ta ci kwallo na biyu daf da za a tashi daga wasan, amma alkalin wasa ya ce an yi satar gida.
Da wannan sakamakon Lazio ta koma ta biyu a kan teburin Serie A, ita kuwa Roma ta zama ta 11 a teburin gasar bana.























