Ban yi nadamar zuwa Man United ba – Sanchez

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan gaba Alexis Sanchez "bai yi nadamar zuwa Manchester United ba" sai dai ya ce bai samu lokaci ba ne mai yawa balle ya nuna kansa.
Dan kasar Chile din mai shekara 30 ya koma Inter Milan ne a matsayin aro har na tsawon kakar wasa guda bayan ya shafe wata 19 a Old Trafford.
Shi ne dan wasan United da ya fi kowa albashi da fan 400,000 duk mako, amma kwallo biyar kawai ya ci tun bayan da ya koma cen daga Arsenal a Janairun 2018.
"Na ji dadin zuwa Manchester United kuma a kodayaushe ina fada cewa su ne suka fi kowa nasara a Ingila," Sanchez ya shaida wa BBC.
"Lokacin da na je Arsenal na ji dadi sosai amma United suna yunkuri suna sayen 'yan wasa domin su ci kofuna.
"Na koma wurinsu ne domin na yi nasara tare da su, ba na nadamar zuwa cen."
Sanchez ya ci wa Arsenal kwallo 80 a wasa 166 bayan zuwansa Emirate kan fan milyan 30 a Yulin 2014.
An saka shi cikin jerin 'yan wasan da za a bai wa kyautar Professional Footballers' Association Players a 2017.
Sai dai komawarsa United ta sa ya gamu da cikas a harkar kwallonsa, inda tauraruwarsa ta disashe.
Kwallo biyu kawai ya ci a wasa 27 a kakar da ta gabata duk da cewa ya yi kokari a kasarsa Chile a gasar Copa America, inda ya taimaka mata zuwa wasan kusa da na karshe da kwallonsa biyu da ya ci.
Wasa 31 kacal aka fara da shi a United cikin 77 kuma 13 kawai aka tashi da shi.
"Ina ganin na fi jin dadi idan ina taka wa kasata leda," in ji shi.
"A Manchester United da sun kyale ni da na yi bakin kokarina. Wani zubin zan yi minti 60 sai a cire ni sannan kuma a ki saka ni a wasa na gaba - ban san dalili ba."



























