Premier ta doke La Liga a tawagar kwararru ta FIFPro

'Yan wasan tawagar Manchester City lokacin da suke murnar lashe gasar Premier ta shekarar 2018/2019
Bayanan hoto, Manchester City ce zakarar Premier cikin shekara biyu a jere
An wallafa

'Yan wasan da ke taka-leda a gasar Premier ne mafiya yawa a cikin jerin sunayen 'yan wasan da za su kasance kwararru 11 na duniya da hukumar FiFPro ta saba fitarwa duk shekara.

Wannan dai shi ne karon farko da aka taba samun yawan 'yan wasan Premier cikin wannan tawagar cikin shekara goma da suka gabata.

Daga cikin sunayen da aka fitar dai akwai 'yan wasa 25 da ke taka-leda a kungiyoyin Ingila, inda suka mamaye na gasar Laliga ta Spaniya.

Bakwai daga cikin yan wasan Liverpool ne suka shiga cikin jerin kwararrun 'yan wasan, duk da cewa 'yan wasan Real Madrid da Barcelona sun fi na Liverpool yawa a cikin tawagar kowannensu.

Za'a sanar da sunayen kwararrun 'yan wasan na duniya ne a ranar 23 ga watan Satumbar bana a birnin Milan na kasar Italiya.

Sama da kwararrun 'yan wasa 23,000 ne da suka fito daga sassan duniya aka bukaci su bayyana kungiya ko kuma dan wasan da yafi burge su.

Kungiyoyin masana harkokin tamaula za su bayyana wanda ya fi iya taka-leda, ko kuma kungiyar da ta fi kwazo daga watan Yulin shekarar 2018 zuwa watan Yulin 2019.

Tawagar karshe da za'a bayyana ta za ta kunshi mai tsaron raga daya da 'yan wasan baya hudu da 'yan wasan tsakiya uku, sai kuma 'yan wasan gaba guda uku.

'Yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool guda hudu suna daga cikin 17 da aka sanya a jerin sunayen farko ciki har da Trent Alexander-Arnold da Andrew Robertson.

Manyan 'yan wasa irin su Romelu Lukaku da David Silva ba su samu kuri'u sosai ba, abin da ya hana su damar shiga cikin jerin kwararrun 'yan wasan karo na biyu a jere.

Tsawon shekara tara Laligar Sifaniya ta dauka tana samar da kwararrun 'yan wasan tawagar, sai dai duk da haka ba ta taba samar da sama da ashirin ba.

Premier ta yi bazata bayan da ta kawo 'yan wasa 21, wanda hakan ne ya sanya ta kawo karshen Laliga.

Bugu da kari, a wancan lokaci Barcelona ce kan gaba wajen samar da kwararrun 'yan wasan.

Barcelona ta samar da yan wasa tara, yayin da Real Madrid ta samar da mutum takwas, sai kungiyoyin Liverpool da Manchester City da suka samar da 'yan wasa bakwai-bakwai kowannensu.

Tsohon dan wasan Real Madrid kuma dan gaban Juventus a yanzu Cristiano Ronaldo shi ne kadai ne sunansa ya fito cikin kwararrun 'yan wasa 11 sau 15 da kungiyar kwallon kafa ta duniya FIFA ta fitar.

"Yan wasan da aka fitar da sunayensu domin zabar kwararru 11:

Masu tsaron raga: Alisson Becker (Liverpool), David De Gea (Manchester United), Ederson Moraes (Manchester City), Jan Oblak (Atletico Madrid), Marc-Andre ter Stegen (Barcelona).

"Yan wasan baya: Jordi Alba (Barcelona), Trent Alexander-Arnold (Liverpool), Daniel Alves (Paris St-Germain/Sao Paulo), Joao Cancelo (Juventus/Manchester City), Daniel Carvajal (Real Madrid), Giorgio Chiellini (Juventus), Virgil van Dijk (Liverpool), Diego Godin (Atletico/Inter Milan), Joshua Kimmich (Bayern Munich), Kalidou Koulibaly (Napoli), Aymeric Laporte (Manchester City), Matthijs de Ligt (Ajax/Juventus), Gerard Pique (Barcelona), Sergio Ramos (Real Madrid), Andrew Robertson (Liverpool), Alex Sandro (Juventus), Thiago Silva (Paris St-Germain), Raphael Varane (Real Madrid), Marcelo (Real Madrid), Kyle Walker (Manchester City).

"Yan wasan tsakiya: Sergio Busquets (Barcelona), Casemiro (Real Madrid), Kevin de Bruyne (Manchester City), Christian Eriksen (Tottenham Hotspur), Frenkie de Jong (Ajax/Barcelona), Eden Hazard (Chelsea/Real Madrid), N'Golo Kante (Chelsea), Toni Kroos (Real Madrid), Arthur Melo (Barcelona), Luka Modric (Real Madrid), Paul Pogba (Manchester United), Ivan Rakitic (Barcelona), Bernardo Silva (Manchester City), Dusan Tadic (Ajax), Arturo Vidal (Barcelona).

"Yan wasan gaba: Sergio Aguero (Manchester City), Karim Benzema (Real Madrid), Roberto Firmino (Liverpool), Antoine Griezmann (Atletico/Barcelona), Harry Kane (Tottenham Hotspur), Robert Lewandowski (Bayern Munich), Sadio Mane (Liverpool), Kylian Mbappe (Paris St-Germain), Lionel Messi (Barcelona), Neymar (Paris St-Germain), Cristiano Ronaldo (Juventus), Mohammed Salah (Liverpool), Son Heung-min (Tottenham Hotspur), Raheem Sterling (Manchester City), Luis Suarez (Barcelona).