Liverpool da kuma Man Utd sun tsayar da shirin sayar da tikitin kallon wasannin badi

Premier League clubs
Bayanan hoto, Kungiyoyin Premier League sun fara shirye-shiryen sayar da tikitin kakar 2020-21 season tickets
An wallafa

Kungiyoyin Premier League da suka hada da Liverpool da Man Utd sun dakatar da shirin sayar da tikitin kallon wasannin badi saboda rashin tabbas a kakar 2020-21 sakamakon cutar korona.

Daf ake da kammala kakar tamaula ta bana kamar yadda aka sayar da tikitin kallon wasannin tun a bara, tuni wasu magoya baya sun fara sayen na kakar badi wasu kuwa yanzu ne za su fara sayen tikitin kakar badi.

Sai dai kuma an dakatar da wasannin kakar bana a cikin watan Maris, saboda tsoron yada cutar korona, kuma har yanzu mahukuntan gasar ba su tsayar da ranar karasa wasannin shekarar nan ba.

Hakan ya sa babu tabbas kan lokacin da za a fara wasannin kakar badi kenan. Ga yadda wasu kungiyoyin Premier suka shirya tunkarar yadda za su sayar da tikitin kallon wasannin badi.

Liverpool

Liverpool, wadda take ta daya a kan teburin Premier da tazarar maki 25 tsakaninta da ta biyu Manchester City ta dakatar da shirin sayar da tikin kallon wasanninta na badi, har sai an samu tabbacin da za a fara kakar 2020-21.

Kungiyar ta ce za ta bude kafar sayar da sabon tikikin kallon wasannin badi da zarrar an sanar da lokacin da za a fara gasar Premier ta badi.

Liverpool ta ce da zarar an amince a karkare kakar bana ta 2019-20 ba tare da 'yan kallo ba za ta biya magoya baya kudinsu, ko kuma wasu su yi masa don su kalli kakar 2020-21 ta tikitin.

Manchester United

Manchester United ta dakatar da kudin farashin tikin bana kuma magoiya bayan kungiyar za su iya sabunta shi, koda ranar 1 ga watan Mayu ce ya kamata a sabunta an kuma dakatar da hakan.

United za ta sanar da ranar sabuntawa da zarar mahukuntan gasar Premier sun tsayar da ranar da za a fara kakar 20-21.

Kungiyat ta kara da cewar idan har za a karkare wasannin da suka rage a Old Trafford ba tare da 'yan kallo ba, kungiyar za ta yi wa magoya baya da musanya ko kuma ta biya kudin yawan wadanda suka rage.

Newcastle United

Newcastle United ta ci karo da kalubale bayan da kungiyar ta kara kudi kan tikin da magoya baya suka saya na kakar 2020-21, duk da cewar ba a tabbatar da ranar fara kakar badi ba.

An caji wasu magoya baya fam 620 ranar Laraba, inda suka ce lamarin abin fargaba mai tsoratarwa.

Kawo yanzu kungiyar ba ta ce komai ba kan lamarin.

Tottenham

Tottenham ta dakatar da sayar da tikitin bana ko kuma sabunta na kakar badi.