Kungiyoyin da ke buga National League sun zabi soke wasannin bana

National League
An wallafa

Kungiyoyin da ke buga National League sun amince a soke kakar kwallon kafa ta bana, nan gaba za a yi tunanin wadanda suka bar gasar da wadanda za su hauro.

Hukumar da ke gudanar da gasar ce ta bukaci kungiyoyin da su amince a karkare kakar kwallon kafa ta bana duk da sauran wasannin da suka rage saboda tsaiko da cutar korona ta haddasa.

Tun a ranar 16 ga watan Maris aka dakatar da wasannin kungiyoyin da ke buga rukuni na biyar da na shida.

Za kuma ayi tunanin yadda ya kamata a samo wadanda za su bar kakar 2019-20 da aka buga da wadanda za su cike gurbinsu.

Kungiyoyi biyu ne daga rukuni na biyar kan shiga League Two, sannan a zubar da hudu a kuma maye gurbinsu da wadda ta lashe National League ta Arewa da ta Kudu da biyun da suka yi nasara a karawar cike gurbi.

A watan Maris aka soke duk wata gasar kwallon kafa ta bana daga rukuni na bakwai zuwa kasa.

John Rooney scores for Barrow