Eric Dier: An tuhumi dan wasan Tottenham da kalubalantar dan kallo

Asalin hoton, Getty Images
An wallafa
Hukumar FA na tuhumar dan wasan Tottenham, Eric Dier, bayan da ya shiga benen 'yan kallo domin ya kalubalanci mai goyon baya a cikin watan Maris
Lamarin ya faru ne a lokacin da Norwich ta fitar da Tottenham daga gasar FA Cup.
Hukumar ta FA na tuhumar Dier da halin rashin da'a wanda ya karya dokar hukumar kamar yadda ta sanar.
Ta kara da cewar bai kyauta ba da halin da ya nuna kuma rashin da'a ne ko kuma kokarin tsoratar wa.
An bai wa dan kwallon nan da 8 ga watan Mayun 2020 domin ya kare kansa.























