Fifa ta bayar da shawarar canja 'yan kwallo biyar a lokacin wasa

Asalin hoton, Getty Images
An wallafa
Kungiyoyi za su fara canja 'yan kwallo biyar a wasa amma na wucin gadi don kawo sauki wajen karkare kakar bana da zarar an ci gaba da wasanni kamar yadda Fifa ta bayar da shawara.
Ana sa ran yin amfani da wannan shawarar na wucin gadi har zuwa karshen kakar 2021.
Hukumar Fifa ta ce ba za a koma wasa kai tsaye ba har sai jami'an lafiya da gwamnatoci sun amince cewar komai ya koma yadda ya kamata.
Cibiyar kungiyar kwallon kafa ta kasa ce wato Ifab keda alhakin amincewa da wannan shawarar da Fifa ta bayar.
BBC ta fahimci cewar Ifab za ta amince da wannan shawarar saboda tun a baya an tattauna kan batun ta yadda za a taimaka wa 'yan kwallo da walwalar su.
Yadda ake son gudanar da tsarin
- A gasar da aka amince a sauya 'yan kwallo uku, za su iya saka biyar jumulla a lokacin wasa.
- Za a yi amfani da tsarin canja 'yan wasa biyar kamar yadda ake yi a lokacin da ake sa uku da kuma lokacin hutu.
- Watakila da yiwuwar saka dan wasa na shida bayan karin lokaci.
- Za a ci gaba da wannan tsarin ga karawa tsakanin tawagar kasa da kasa har zuwa 31 ga watan Disambar 2021.























