Ranar Litinin ake sa ran 'yan wasan kungiyoyin Serie A za su fara atisaye

Serie A
Bayanan hoto, 'Yan wasan Juventus a lokacin da suke yin atisaye
An wallafa

Ranar Litinin ake sa ran 'yan wasan da ke buga gasar Serie A za su fara atisaye a shirin da ake yi na karkare wasannin 2019-20.

A makon jiya Firai Ministan Italiya, Giuseppe Conte ya ce 'yan wasa daidaiku za su fara atisaye ranar 4 ga watan Mayu, sannan kungiyoyi su fara motsa jiki ranar 18 ga watan.

Haka ma Ministan wasanni Vincenzo Spadafora ya ce 'yan wasan da ke tsalle-tsalle da guje-guje za su fara motsa jiki a daidaiku, sannan na kungiyoyi su fara atisaye ranar 18 ga watan.

Sai dai jawabin Spadafora ya jawo cece-kuce, inda ranar Asabar kungiyar da ke buga Serie A, Sassuolo ta ce za ta bar 'yan wasanta su yi amfani da wurin atisayenta ranar Litinin.

Bologna wadda ke yankin Emilia Romagna an ba ta kulawa ta musamman, inda aka amince 'yan wasan tsalle-tsalle da guje-guje da 'yan kwallo su yi atisaye a daidaiku ranar 4 ga watan Mayu, sannan su fara cikin rukuni ranar Talata.

An kuma amince a mota jiki a yankin Campania, inda ya hada da Naples, sai dai kawo yanzu Napoli ba ta ce komai ba.

Tun farko gwamnatin Italiya ta amince masu sana'ar tsalle-tsalle da guje-guje da masu motsa jiki don neman lafiya su rinka yin atisaye amma a daidaiku da kuma bayar da tazara don gudun yada cutar korona.

Ranar 9 ga watan Maris aka dakatar da gasar Serie A, koda yake hukumar kwallon kafar Italiya da masu gudanar da gasar lik din kasar na sa ran karkare kakar bana.

Sai dai kuma har yanzu gwamnatin Italiya ba ta fayyace ko za ta bari a ci gaba da gasar Serie A ta 2019-20 ko akasin hakan.