Rashford ya gwanance a fannin tamaula — Maguire

Maguire and Rashford
An wallafa

Dan wasan Manchester United, mai tsaron baya Harry Maguire ya ce bai taba yin wasa da dan kwallon da ya gwanance a fannin tamaula kamar Marcus Rashford ba.

Rashford mai shekara 22 na taka rawar gani a kakar bana karkashin koci Ole Gunnar Solskjaer, har zuwa lokacin da ya ji rauni a watan Janairu.

A cikin watan Maris aka dakatar da wasannin Premier don gudun yada cutar korona, hakan zai bai wa Rashford damar murmurewa kafin a ci gaba da wasannin shekarar nan cikin watan Yuni.

Tuni dai Maguire ya kwatanta Rashford da cewar matashin dan kwallon kafa ne da babu kamarsa a wannan lokacin.

An tambayi Maguire ko yana ganin nan gaba Rashford zai iya zama kyaftin din Manchester United sai ya ce ''Sosai kuwa yana da kokari sosai''.

''Rashford yana mai da hankali a lokacin da yake murza leda yana kuma da kwazo za a iya dogara da shi a duk lokacin da ake wasanni.''

Rashford ya ci kwallo 19 a dukkan fafatawar da ya yi a bana, kafin ya yi rauni a Janairu, ya kuma zama matashin dan wasa na hudu da ya ci wa kungiyarsa kwallo 200.

Matasa uku da suka yi wannan bajintar sun hada da Norman Whiteside da George Best da kuma Ryan Giggs.