Deeney: Ina jin tsoron koma wa horo

Asalin hoton, Getty Images
An wallafa
Kyaftin din Watford, Troy Deeney ya ce ba zai koma horo ba saboda fargabar hakan zai iya shafar iyalansa saboda annobar korona.
A ranar Talata ne 'yan wasan gasar Firemiya suka soma horo kafin a koma fagen tamaula.
Deeney ya ce diyansa na fama da matsalar nunfashi kuma shiga tamaula na iya ta'azara ciwon da yaron ke fama da shi.
Akwai matukar damuwa cewa cutar korona ba ta yi wa bakar fata da sauki.
'Ya kamata mu koma a wannan makon, amma na ce ba zan koma ba,' in ji Deeney.
Bayanai sun nuna cewa Watford ba ta da wata damuwa kan matakin da Deeney ya dauka.























