Son Heung-min ya koma Tottenham bayan kammala aikin soja

Son Heung-min
Bayanan hoto, Son ya yi fice a fagen harbin bindiga kuma yana kan gaba a cikin mutum 157 da suka yi wa kasa aikin horon soji
An wallafa

Dan kwallon Tottenham, Son Heung-min ya koma Ingila, bayan da ya gama aikin soja da ya zama na tilas don bautawa kasarsa Koriya ta Kudu.

Son ya yi mako uku a rundunar sojin Koriya ta Kudu, inda ya kammala horo cikin mutane biyar da suka fi kwazo.

Son mai shekara 27, ba ya bukatar a killace shi bayan da ya koma Ingila, tunda ba a sameshi da cutar korona ba, saboda haka zai iya yin atisaye tare da 'yan wasa.

Dan wasan zai iya fara atisaye na daidaiku da sanyin safiyar Litinin.

Dan wasa shi kadai zai iya yin atisaye kamar yadda gwamnati ta bukata a shirin da ake na ci gaba da gasar Premier ta bana da matakan hana yada annobar.

Son ya yi jinyar karayar hannu wanda aka ce ba zai kara buga wasanni ba sai badi, amma cutar korona ta tsayar da gasar Premier a cikin watan Maris.

Dan wasan ya yi wa kasarsa bauta ba tare da hakan ya shafi sana'arsa ta kwallon kafa ba.

Son yana buga wa kasarsa kwallon kafa hakan ne ya sa bai yi aikin soja na wata 21 ba, ya kuma lashe Asia Games a 2018 shi ya sa ya yi mako uku a aikin sojan.