''Wasu kwararrun 'yan kwallo na shan wuya a lokacin cutar korona''

Food Distribution
An wallafa

Wasu 'yan wasan Latin Amurka da na Afirka na dogara da abincin da ake rabawa don su samu su koshi in ji hukumar kwararrun 'yan kwallo ta duniya, FIFPRO.

Hukumar ta kara da cewar wasu kwararrun 'yan wasan kan sha wahala kan su samu abinci, yayin da wasu kasashe ke shirin ci gaba da gasar bana, ba tare da gwajin 'yan kwallo ba.

Bayan da wasu kasashen ke yunkurin karkare kakar tamaula ta shekarar nan, hukumar wadda ke da mambobin kasashe 65 a duniya ta ce ya zama wajibi a yi nazarin matsin da 'yan kwallo za su fada idan ba matakan kariya.

Janar sakatare na hukumar, Jonas Baer-Hoffmann ya ce rashin wakiltar wasu 'yan kwallo zai iya jefa su cikin matsi a irin wannan lokacin na mawuyacin halin annoba.

Ya kara da cewar mambobinta bakwai da suka hada da Colombia da Paraguay da Uruguay da Honduras da Panama da Botswana da kuma Masar na ciyar da 'yan kwallo ''saboda ba su da hali, kudin da suke da shi bai taka kara ba wato albashi.''

Ya kara da cewar a wasu kasashen da ke ta kokarin ci gaba da gasar bana da tuni suka fara atisaye za su iya barin baya da kura.

Baer-Hoffmann ya kuma ce wasu ba sa tanadar kayayyakin gwaji a kokacin ci gaba da gasa, kuma hakan ka iya yada cutar korona, amma sun tanadi kayan gwaji da za su rabawa mambobi.

Ya kuma ce da daman 'yan wasa ba su da abinci kuma babu yadda za su yi, saboda haka ko an bukaci su koma tamaula duk da fargabar annonbar babu yadda za su yi haka za su bi umarni.

A ranar Asabar aka ci gaba da gasar Bundesliga ba tare da 'yan kallo ba, kuma a watan gobe ne ake sa ran ci gaba da wasannin Premier League.