A ranar 20 ga Yuni za a ci gaba da gasar Serie A ta Italiya

Asalin hoton, Getty Images
An wallafa
Manyan gasannin ƙwallon ƙafa biyu na Turai sun sanar da shirye-shiryensu na ci gaba da wasanni a watan gobe.
Ministan wasannin Italiya, Vincenzo Spadafora ya ce za a ci gaba da karawa a babbar gasar ƙasar ta Serie A ranar 20 ga watan Yuni.
Ya ce yana fata za a yi karawa ta biyu a zagayen daf da ƙarshe na cin kofin Italiya mako guda kafin nan.
Ƙungiyoyi biyu ne daga Milan, ɗaya daga cikin biranen Italiya da suka fi fama da annobar korona, har yanzu ke cikin gasar.
Tun da farko, Gasar Firimiyar Ingila ta bayyana cewa za a ci gaba da wasanni ranar 17 ga wata, amma bisa amincewar gwamnati.























