Ethan Ampadu: Dan wasan zai koma tamaula a RB Leipzig bayan ya gama jinya

Asalin hoton, Huw Evans agency
Dan wasan Wales Ethan Ampadu yana dab da komawa ganiyarsa bayan da aka soma gasar Bundesliga ba tare da ya buga wa RB Leipzig wasa ba.
Ampadu, dan shekara 19, yana zaman aro a kungiyar ta Jamus daga Chelsea.
Bai buga wasa ko daya ba tun bayan da aka koma buga gasa ba tare da 'yan kallo ba sakamakon annobar korona a watan Mayu saboda ciwon baya.
Sai dai Leipzig ta ce a hankali yana "sake komawa atisaye" kuma yana bin tsarin da aka gindaya masa.
Leipzig iat ce ta uku a saman teburin gasar Bundesliga kuma za ta fafata da Paderborn ranar Asabar.
Ampadu ya yi ta faman ganin an sanya shi a wasa tun da ya koma Leipzig daga Stamford Bridge a bazarar da ta wuce, amma ya taka rawar gani a gasar zakarun Turai lokacin da suka doke Tottenham kafin barkewar annobar korona.
Fafatawar wacce suka yi nasara da ci 1-0 a watan Fabrairu ita ce lokacin karshe da Ampadu ya murza leda kafin ya ji rauni.























