Depay ya koma atisaye a Lyon bayan jinyar wata shida

Memphis Depay
An wallafa

Memphis Depay ya koma yin atisaye a kungiyarsa ta Olympique Lyon kamar yadda ta sanar.

Wannan ne karon farko da dan kwallon tawagar Netherlands ya fara taka leda tun bayan jinyar wata shida da ya yi.

Mai shekara 26 tsohon dan wasan PSV Eindhoven da Manchester United ya ji rauni ranar 15 ga watan Disamba a gasar Ligue 1 Da Stade Rennes.

Ranar Litinin Depay ya je Lyon don likitoci su auna koshin lafiyarsa don ci gaba da karbar horon tamaula da tuni Lyon ta fara atisaye a makon jiya.

Kungiyar na shirin fafatawa a gasar Champions League da za a ci gaba, inda ta ci Juventus 1-0 a wasan farko na zagayen kungiyoyi 16 da suka rage a wasannin.

Komawa atisaye da Depay ya yi batu ne da zai karawa Lyon kwarin gwiwa, wanda ya ci kwallo tara a Ligue 1 ta Faransa.

Ya zuma zura biyar a raga a gasar Champions League da ya buga a kakar bana tun kan ya ji rauni.