Dele Alli: An dakatar da dan wasan kan kalaman da yi game da cutar korona

Asalin hoton, Getty Images
Dele Alli ba zai buga wa Tottenham karawar da za ta yi da Manchester United ba, bayan da aka dakatar da shi wasa daya kan kalaman da ya yi a shafinsa na sada zumunta kan cutar korona.
Alli, mai shekara 24 ya yi wani bidiyo a kafar sada zumuntarsa a Snapchat a watan Fabrairu inda ya yi barkwanci kan bullar annobar da zolayar mutanen Asiya.
An ci tarar dan kwallon tawagar Ingila fam 50,000, an kuma umarce shi da ya nemi ilimin da za a kara wayar da shi kan halin da ya aikata.
Ba zai buga wasan da Tottenham za ta karbi bakuncin Manchester United a gasar Premier ranar 19 ga watan Yuni ba.
Ranar 17 za a ci gaba da gasar cin kofin Premier ta bana, wadda aka dakatar tun cikin watan Maris saboda bullar cutar korona.
Za kuma a ci gaba da wasanni ne ba 'yan kallo don gudun yada annobar.
Liverpool ce ke kan gaba a teburi da tazarar maki 25 tsakaninta da Manchester City ta biyu.
Wannan ne karon farko da Liverpool ke fatan lashe kofin Premier League a karon farko tun bayan shekara 30.



























