Bellingham ya kusa kammala kulla yarjejeniya da Dortmund

Asalin hoton, Reuters
An wallafa
Borussia Dortmund na gabda kammala kulla yarjejeniya da matashin dan kwallon Birmingham City, Jude Bellingham.
A cikin watan Agusta, Bellingham ya kafa tarihin kasancewa dan kwallo mafi karancin shekaru da ya buga wa Birmingham a cikin shekaru 38.
BBC ta fahimci cewa zai kulla yarjejeniyar shekaru biyar a kan fam miliyan 20 domin komawa murza leda a Jamus.
Kungiyar Manchester United ta nuna sha'awar sayen dan kwallon amma bisa dukkan alamu hakan zai yi wuya a yanzu.
Amma sai Dortmund ta ja ra'ayinsa gannin yadda Jadon Sancho ya bar Manchester City ya koma Jamus kuma ya haskaka sosai.























