Damben da Taufik ya buge Autan Dutsen Mari a Abuja

Bayanan bidiyo, Damben da Taufik ya buge Autan Dutsen Mari a Abuja
An wallafa

A turmi na biyu Taufik dogon Ebola daga Kiudu ya kashe Autan Dutsen Mari Guramada a damben safiyar da aka yi a DeiDei da ke Abuja, Najeriya.

  • Sauran wasannin da aka buga musamman da suka yi kisa:
  • Bahagon Buhari ya kashe Ginshikin Mai Takwasara
  • Shagon Dan Matawalle ya buge Shagon Sawun Kura
  • Bahagon Shagon Alabo ya doke Dogon Inda
  • Dan Katsina ya yi nasara a kan Shagon Bahagon Buma

Sai dambatawar da aka tashi canjaras

  • Ginshikin Mai Takawasa da Dan Mutan Karmu
  • Shagon Mu'azu da Shagon Sawun Kura
  • Balan Kwarkwada da Bahagon Musan Kaduna