Real Betis ta nada Pellegrini a matsayin kocinta

Asalin hoton, Getty Images
Kungiyar da ke buga La Liga, Real Betis ta nada tsohon wanda ya ja ragamar West Ham United da Manchester City, Manuel Pellegrini a matsayin sabon kocinta.
Pellegrini, wanda ya taba horar da Real Madrid da Villareal da kuma Malaga dukkansu a Spaniya, ya rasa aikinsa, bayan da West Ham ta sallameshi a cikin watan Disamba.
Kwantiragin dan kasar Chile mai shekara 66 zai kare da Real Betis a karshen kakar 2023.
Pellegrini ya lashe kofin Premier League tare da Manchester City a kakar 2013-14 da EFL biyu a kaka ukun da ya yi a Etihad.
Pellegrini zai maye gurbin Rubi wanda aka sallama ranar 21 ga watan Yuni, bayan da Athletic Bilbao ta doke Real Betis a gasar La Liga.
Daraktan wasannin kungiyar, Alexis Trujillo zai ci gaba da jan ragamar kungiyar zuwa karshen kakar bana.























