Kamaru Usman: Bayanai biyar kan damben Kamara Usman da Jorge Masvidal

Asalin hoton, Kamara Usman
Kamaru Usman zai gwada kwanji da Jorge Masvidal ranar Lahadi 12 Yuli domin kare kambunsa na ajin welterweight.
Kamata ya yi Usman ya kara da Gilbert Buns amma saboda cutar korona da ya kamu da ita, hakan ba ta samu ba lamarin da ya sa cikin kankanin lokaci Masvidal ya maye gurbinsa.
Shugaban gasar damben UFC Dana White ne ya ba da shawarar a gudanar da gasar a wani sabon wuri domin ba shi damar shirya wasa yayin da ake fama da annobar korona.
Rahotanni na cewa 'yan dambe da dama ba su da izinin shiga Amurka saboda takunkumin tafiye-tafiye, White kuwa ya karkata akalarsa zuwa tsibirin Yas da ke Abu Dhabi.
Ga abubuwa biyar da ya kamata ku sani game da damben Kamaru da Misvidal.

Asalin hoton, Getty Images
Ina ne wajen damben UFC?
Wurin damben na nan a tsibirin Yas a Abu Dhabi.
Ba wannan ne karon farko da ake gudanar da harkokin wasanni a tsbirin ba, waje ne da aka saba tseren motocin Formula 1.
Warner Bros World, Ferrari World, Yas WaterWorld da Yas Marina Circuit duk wurare ne da ke cikin tsibirin.
Tsibirin zai kasance cikin dokar kulle yayin da ake gudanar da wasan UFC sannan za a tabbatar da tsaron rayukan mutane.
Wane lokaci Kamaru zai fafata da Masvidal?
Mutanen da ke wajen Najeriya za su iya kallon wasan a tashar Supersports 11 a DSTV ranar Lahadi tsakanin karfe 5 zuwa 7 na safe.

Asalin hoton, Getty Images
Wane tarihi 'yan damben suka kafa?
Usman na kokarin ci gaba da haskawa. Sau daya ya yi rashin nasara a hannun Jose Caceres a damben da suka yi cikin shekarar 2013.
A lokuta da dama kuma Usman ya yi galaba kan wasu manyan 'yan dambe. Ya yi nasara kan Covington da Woodley da Rafael dos Anjos da Demian Maia.
KAMARU USMAN
Kambu: 16-1-0
Nasarori: 16
Dokewa ta hanyar sili daya kwale: 7
Ta hanyar mika wuya: 1
Ta hanyar yanke shawara: 8
Canjaras: 0
Rashin nasara: 1
JORGE MASVIDAL
Shekara: 35
Tsayi: 5ft 11in
Reach: 74 inches
Kambu: 35-13-0
Nasarori: 35
Dokewa ta hanyar sili daya kwale: 16
Ta hanyar mika wuya: 2
Ta hanyar yanke shawara: 17
Canjaras: 0
Rashin nasara: 13
Wane ne Masvidal?
Masvidal ya fito ne daga Miami da ke Florida a Amurka. Ya fara koyon dambe tun yana karami.
Bayan da ya daina zuwa makaranta, ya yanke shawarar neman kwarewa a dambe. A shekarar 2013, ya kulla yarjejeniya da UFC inda kuma ya yi nasara kan Tim Means. Dan damben mai shekara 35 ya yi kaurin suna a wasan dambe.
UFC 251: Wasannin da za a fafata
Kamaru Usman da Jorge Masvidal - Welterweight
Alexander Volkanovski da Max Holloway - Featherweight
Petr Yan da Jose Aldo - Bantamweight
Jessica Andrade da Rose Namajunas - Gasar Strawweight ajin mata
Amanda Ribas da Paige VanZant - Gasar Flyweight ajin mata



























