Autan Dutsen Mari ya buge Bahagon Musa da Shagon Inda

Bayanan bidiyo, Autan Dutsen Mari ya buge Bahagon Musa da Shagon Inda
An wallafa

An dambata da dama a wasan safe da aka yi a gidan damben Ali Zuma da ke Dei-Dei a Abuja, Najeriya ranar Lahadi.

Damben da aka yi kashe-kashe sun hada da:

  • Guguwar Mai Takwasara Guramada ya buge Dan Mutan Karmu daga Jamus
  • Shagon Matawallen Kwarkwada daga Kudu ya doke Shagon Shamsu daga Arewa
  • Shagon Bahagon Buma Guramada ya yi nasara a kan Shagon Mahaukaci Teacher daga Arewa
  • Autan Dutsen Mari Guramada ya kasge Garkuwan Musan Kaduna daga Jamus
  • Autan Dutsen Mari Guramada ya buge Shagon Inda daga Arewa

Damben da bai yi kisa ba kuwa:

  • Shagon Shagon Buzu daga Arewa da Shagon Autan Faya daga Kudu
  • Shagon Habu Jos daga Arewa da Guguwar Mai Takwasara Guramada
  • Shagon Dan Katsinawa daga Jamus da Shagon Shagon Bahagon Kanawa daga Kudu